A ranar Juma'a 7 ga Oktoba, 2016 ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad Elrufa'i ya fitar da umurni, inda ya shelanta cewa ya haramta Harkar Musulunci a Najeriya, kuma za a garkame duk wani mabiyin Harkar Musuluncin da aka kama na tsawon shekaru bakwai a gidan Yari. Ya bayyana cewa fadar Gwamnatin Jihar ta Kaduna ce ta cimma matsaya a kan zartar da wannan mataki bisa la'akari da shawarwarin da Hukumar Binciken kisan kiyashin da Jami'an tsaro Sojojin Najeriya suka yi a garin Zariya a cikin watan Disambar shekarar 2015 da ta gabata ta bayar.
Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) tana shelanta wa daukacin al'umma da babbar murya cewa ba ta aminta da wannan umurni da Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar ba, kuma tana kallon umarnin a matsayin take hakki da kuma 'yanci da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba mu a matsayinmu na 'yan Kasa na iya shelanta ra'ayinsu da kuma gudanar da taro ba tare da tsangwama ba. Kuma wannan lamari ba wani abu ba ne illa wani makirci na Gwamna Nasir Elrufa'i na ci gada da aiwatar da ajandar yin kisan kiyashi a kan fararen hula 'yan Najeriya wanda ya fara a cikin watan Disambar shekarar 2015 da ta gabata.
Dukkanin hujjojin da aka ambata domin nuna dacewar wannan doka ba daidai suke ba kuma ba gaskiya ba ne. Abin mamaki ne Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da shawarwarin da Hukumar Bincike ta bayar, alhali kuma ta yi gum da bakinta, ta ki cewa komai a kan cin zarafi da kuma take hakkin bil'adama da Rahoton Hukumar Binciken ya tabbatar da an aikata, wadanda suka hada da kisan babu gaira babu dalili na mutane 347 a lissafinsu da kuma bizne su a boye a cikin rami daya ba tare da izinin dangin mamatan ba. Don me ta ki yin magana a kan shawarar da Hukumar Binciken ta bayar na hukunta jami'in Sojojin da suka jagorancin kaddamar da harin kisan kiyashin a garin Zariya? Don haka ba za a yaudare mu da wannan matsaya ta munafunci ba ta Gwamna Nasir ElRufa'i.
Gwamnati ta kasa tabbatar da dacewar ci gaba da tsare Jagoranmu, ta kuma kasa nuna dacewar harin da ta kaddamar, don haka ne ya zama yanzu babu wani abu da za ta iya yi illa kame-kame da kuma karya da karairayi. Don haka muna son mu ankarar da wadanda suka bayar da wannan umurni wanda ba ya bisa ka'ida cewa, su sani Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ba Kungiya ba ce ko taron Jama'a, al'amari ne fahimtar addini na duniya gaba daya (global concept) wanda kuma ba a iya murkushe shi ta hanyar bayar da umurnin tilasci. Saboda haka ba za a iya taka mana burki ba ta hanyar wannan mataki na wauta. Sahihin hankali, tunani, dokoki da kuma kundin tsarin Mulki, ma'abota hankali da kuma sahihin tunani dukkaninsu suna goyan bayan Harkar Musulunci a Najeriya. Don haka babu wanda ya isa ya hana mu 'yancinmu a daidaiku ko gungun mutane na yin bauta da kuma gudanar da taro.
Mu na so mu shelanta tare kuma da tabbatar wa da daukacin al'umma cewa wannan mataki da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka ba zai sanya mu mu aikata wani aiki na hatsaniya ko rashin dacewa ba, kamar yadda Gwamnatin take tunanin sanya mu mu yi. Za mu kalubalanci wannan lamari ne ta hanyar bin matakai na lumana da kuma shari'a, kamar yadda muka saba yi tun tsawon kimanin shekaru Arba'in da suka gabata. Za mu ci gaba da bin matakai na lumana da kuma Shari'a don ganin an yi adalci a kan kisan kiyashin da aka kaddamar a garin Zariya a cikin watan Disambar shekarar 2015 da ta gabata.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
08050786093
08/10/2016
Fassara daga Zaharaddeen Sani Malumfashi
08068322437